(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

2. Zunubi Ya Shigo Cikin Duniya

Image

Adamu da matarsa, Hawwa'u, suna jin daɗin rayuwa a cikin gonar inda Allah ya sa su. Dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba domin babu zunubi a cikin duniya. Su kan yi tafiya cikin gonar, suna kuwa magana da Allah.

Image

Amma akwai maciji mai wayo a cikin gonar. Ya tambayi macen, "Ko Allah ya ce, 'ba za ku ci daga ƴaƴan itacen cikin gonar ba?'"

Image

Macen ta amsa ta ce, "Allah ya ce muna iya cin dukan ƴaƴan itace banda ƴaƴan icce sanin nagarta da mugunta. Allah ya ce mana 'Idan kun ci ƴaƴan iccen nan, ko kuka taɓa shi, za ku mutu.'"

Image

Macijin ya cewa macen, "Ba gaskiya ba ne! Ba za ku mutu ba. Allah ya san da in kun ci za ku zama kamar Allah, za ku kuma san nagarta da mugunta kamar yadda ya sani."

Image

Macen ta gani ƴaƴan iccen yana da kyau, zai yi daɗin ci, sai ta cira ta ci. Sai ta baiwa mijinta, da yake tare da ita, shi ma ya ci.

Image

Nan da nan sai idanunsu suka buɗe, sai suka gane tsirara suke. Sai suka samo ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.

Image

Mutumen da matarsa suka ji motsin Allah yana yawo a gonar, sai suka ɓoye wa Allah. Amma Allah ya kira mutumen, "Ina kake?" Adamu ya amsa, "Na ji motsinka cikin gonar, na ji tsoro domin tsirara nake, na kuwa ɓuya."

Image

Sai Allah ya tambaye shi, "Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga ƴaƴan iccen da na ce kar ka ci?" Mutumen ya amsa, "Macen da ka ba ni itace ta ba ni na ci." Sai Allah ya tambayi macen, "Me kika yi haka?" Macen ta amsa ta ce, "Macijin ne ya yaudareni."

Image

Allah ya cewa macijin, "Ka zama la'ananne! Za ka yi rarrafe, za ka ci turɓaya. Zan sa ƙiyayya tsakanin kai da macen, ƴaƴanka da ƴaƴanta kuma za su yi ƙiyayya. Zuriyar macen za ta ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje diddigensa."

Image

Allah ya cewa macen, "Zan tsanenta naƙudarki ainun; muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallakeki."

Image

Allah ya cewa mutumen, "Ka kasa kunne ga matarka ka tayar mani. Yanzu ƙasa ta la'antu, da wahala za ka yi aiki ka samu cimaka. Za ka mutu, jikinka kuma zai koma turɓaya." Mutumen ya sa wa matar suna Hawa'u, wato mai bada rai, gama za ta zama uwar dukan mutane. Sai Allah ya yi wa Adamu da Hawa'u sutura da fatar dabbobi.

Image

Sai Allah ya ce, "Yanzu mutane sun zama kamar mu, sun san nagarta da mugunta, bai kyautu ba su ci kuma ƴaƴan icce na rai, su rayu har abada." Allah ya kori Adamu da Hawa'u daga gonar Aidan. Allah ya kafa kerubobi da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.

Labarin LMT daga Farawa 3