(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

38. An Ci Amanar Yesu

Image

Kowace shekara Yahudawa suna sallar Idin Ƙetarewa. Wannan Idin suna yin shi don tunawa da yadda Allah ya kuɓutar da kakanninsu daga bauta a Masar ƙarni da yawa da suka wuce. Kusan shekara uku bayan da Yesu ya fara wa'azi da kowaswa a fili, Yesu ya faɗawa almajiransa cewa yana so ya ci Idin Ƙetarewa tare da su a Urshalima, kuma za a kashe shi a can.

Image

Ɗaya daga cikin almajiran Yesu yana da sunan Yahuda. Yahuda yana riƙe da jikar kuɗin manzani, amma yana da son kuɗi a zuciya, kuma yana satar kuɗi daga cikin jikar. Bayan da Yesu da almajiransa suka iso Urshalima, Yahuda ya je ganin shugabannin addini Yahudawa, kuma ya bada kansa domin cin amanar Yesu a maimakon kuɗi. Yana sane da cewa shugabannin Yahudawa sun yi musun Yesu ne Almasihu, kuma sun tsara su kashe shi.

Image

Shugabannin Yahudawa, tare da babban firist, suka biya Yahuda kuɗi tamma talatin don ya ci amanar Yesu. Wannan ya faru kamar yadda annabawa suka faɗa. Yahuda ya yarda, ya ƙarɓi kuɗin, kuma ya tafi. Ya fara neman halin da zai taimaka a kama Yesu.

Image

Cikin Urshalima, Yesu ya ci Idin Ƙetarewa da almajiransa. Sa'ad da suke cin Idin Ƙetarewa, Yesu ya ɗauki gurasa ya gutsutsura, Ya ce, "Ku ɗauka ku ci. Wannan jikina ne da an bayar dominku. Yi wannan domin tunawa da Ni." Haka nan, Yesu ya faɗa cewa jikin za a miƙa shi hadaya dominsu.

Image

Sai Yesu ya ɗauki ƙoƙon, kuma ya ce, "Ku sha. Jinina ne na Sabon Alkawali da aka zubas domin gafarar zunubai. Ku yi wannan domin tunawa da Ni kowane loton da ku ka sha shi."

Image

Sai Yesu ya cewa almajiransa, "Ɗaya daga cikinku zai bashe Ni." Almajiran suka damu, kuma suka yi tambaya wane ne zai yi wannan abu. Yesu ya ce, "Mutumen wanda zan baiwa guntun burodi shi ne maci amana." Sai ya baiwa Yahuda burodin.

Image

Bayan da Yahuda ɗauki burodin, Shaiɗan ya shiga cikin shi. Yahuda ya fita, kuma ya tafi ya taimaki shugabanin Yahudawa su kama Yesu. Cikin dare ne.

Image

Bayan abincin, Yesu da almajiransa suka tafi zuwa dutsen Zaitun. Yesu ya ce, "Za ku yashe ni da dare. A rubuce yake, "Zan bugi makiyayi, kuma dukan tumaki za su watse."

Image

Bitrus ya amsa ya ce, "Ko duka sauran sun yashe ka, ni ba zan bari ba!" Sai Yesu ya cewa Bitrus, "Shaiɗan yana bukatar dukanku, amma na yi addu'a dominku, Bitrus, don kada bangaskiyar ka ta ɓace. Hakika da daren nan, kafin zakara ya yi cara za ka yi musun sanina sau uku."

Image

Sai Bitrus ya cewa Yesu, "Hakika, ko da zan mutu, ba zan yi musun ka ba!" Duka sauran almajiran suka faɗi haka.

Image

Sai Yesu ya tafi tare da almajiransa wani wuri da ake kira Gatsemani. Yesu ya umurci almajiransa su yi addu'a don kada su faɗa cikin jaraba. Sai Yesu ya tafi shi kaɗai yin addu'a.

Image

Yesu ya yi addu'a sau uku, "Uba, idan ya yiyu, kada ka bari in sha wannan ƙoƙo na wahala. Amma in babu wata hanya domin mutane su samu gafarar zunubainsu, to bari nufinka ya cika, "Yesu ya damu ƙware har jiɓin jikinsa suna kama da jiɓin jini. Allah ya aike da mala'ika ya ƙarfafa shi.

Image

Bayan kowane lokacin addu'a, Yesu yana komawa ga almajiransa, amma suna barci. Da ya sake komawa kari na uku, Yesu ya ce, "Ku tashi! Mai bashe ni ya zo."

Image

Yahuda ya zo da shugabannin Yahudawa, da sojoji, kuma da taron jama'a. Suna ɗauke da takuba da kulake. Yahuda ya zo wurin Yesu ya ce, "Gaisuwa, Malam," kuma ya sumbace shi. Wannan ne alamar da shugaban Yahudawa za su kama shi. Sai Yesu ya ce "Yahuda, ko ka bashe ni da sumba?"

Image

Sa'ad da sojojin suka kama Yesu, Bitrus ya zare takobinshi ya yanke kunne ɗaya daga barorin babban firist. Yesu ya ce, "Maida takobinka! Ina iya tambayar Ubana rundunar mala'iku su kare ni. Amma zan yi biyayya da Ubana." Sai Yesu ya warkar da kunnen mutumen. Bayan da aka kama Yesu, duka almajiran sun watse.

Labarin LMT daga Matiyu 26: 14-56; Markus 14:10-50; Luka 22:1-53; Yahaya 12:6; 18: 1-11