(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

14. Ragaita Cikin Jeji

Image

Bayan da Allah ya faɗa ma Isra'ilawa dokokin da yake so su yi biyayya da su kamar alkawalin sa, sun tafi daga dutsen Sinai. Allah ya ci gaba da bida su zuwa ƙasar alkawali wanda ake kira ƙasar Kan'ana. Al'amudin girgije ya shiga gaban su zuwa Kan'ana, sai suka bishi.

Image

Allah ya yi wa Ibrahim, Ishaƙu da Yakubu alkawalin zai basu ƙasar alkawali da su da zuriyarsu, amma yanzu akwai mutane da yawa a ƙasar. Ana kiransu Kan'aniyawa. Kan'aniyawa ba su san Allah ba. Suna bauta wa waɗansu alloli daban, kuma sun cika da aikata zunubi.

Image

Allah ya faɗawa Isra'ilawa, "Sai kun kori Kan'aniyawa daga ƙasar alkawali. Kada ku yi cuɗanya da su, kada ku aure su. Ku hallaka dukan gumakansu. Idan ba ku yi mini biyayya ba, za ku bauta ma gumakansu maimakona."

Image

Sa'ad da Isra'ilawa suka kai iyakar Kan'ana, Musa ya zaɓi mutum goma sha biyu, ɗaya daga cikin kowace kabilar Isra'ila. Ya ba su umurnin su je su yi leƙen asirin ƙasar su ga yaya take. Su kuma yi leƙen asirin Kan'aniyawa su gani ko masu ƙarfi ne ko maras ƙarfi ne.

Image

Mutanen goma sha biyu suka yi tafiya cikin Kan'ana kwana arba'in, sai suka komo. Suka cewa mutane, "Ƙasar tana da ni'ima sosai da kuma amfani mai ɗumbin yawa! Amma goma daga cikin ƴan leƙen asirin suka ce, "Garuruwan ƙarfafa ne, kuma mutanen manya ne! Idan muka faɗasu za su ci mu da yaƙi hakika!"

Image

Nan da nan Kaleb da Joshuwa, da sauran ƴan leƙen asirin suka ce, "Da gaske ne mutanen Kan'ana masu tsawo ne, kuma suna da ƙarfi, amma muna iya cin su da yaƙi! Allah zai yi kokawa domin mu!"

Image

Amma matanen ba su ji abin da Kaleb da Joshuwa suka faɗa ba. Sun yi fushi da Musa da Haruna, suka ce, "Me ya sa kuka kawo mu cikin wannan matsanancin wuri? Daman mun yi zamanmu a Masar, da a kashemu a yaƙi, matanmu da yaranmu su zama bayi." Mutanen sun so su zaɓi wani jagora ya mayas da su Masar.

Image

Allah ya husata sosai, sai ya sauko cikin alfarwa ta taruwa, ya ce, "Domin kun yi mini tawaye, dukan mutanen za su yi yawo cikin jeji banda Joshuwa da Kaleb, duk wanda yake da shekara ashirin ko hiye zai mutu, ba zai shiga ƙasar alkawali ba."

Image

Da mutanen suka ji haka, sai suka ƙommace da ba su yi zunubi ba. Sai suka ɗauki makamensu, suka je suka faɗa Kan'aniyawa da yaƙi. Musa ya faɗake su kada su je domin Allah ba ya tare da su, amma ba su kasa kunne gare shi ba.

Image

Allah bai tafi tare da su ba cikin yaƙi ba, sai aka ci su da yaƙi, da yawa suka mutu. Sai Isra'ilawa suka juwa baya daga Kan'ana, suka yi yawo cikin jeji har shekara arba'in.

Image

Cikin waɗannan shekaru arba'in da mutanen Isra'ila suka yi yawo cikin jeji, Allah ya tanada komi dominsu. Ya basu gurasa daga sama, da ake kira "manna." Ya kuma aiko da maƙware (kamar tsuntsaye madaidaita) cikin wurin zangunansu don su samu abinci. Cikin dukan wannan lokacin Allah ya tsare kayan jikinsu da takalmansu daga ɓaci.

Image

Allah ya yi al'ajabin huddo masu ruwan sha daga dutse. Amma duk da wannan, mutanen Isra'ila sun yi ta gunaguni a gaban Allah, da gaban Musa. Duk da haka nan Allah ya riƙe alkawalin da yi wa Ibrahim, Ishaƙu da Yakubu.

Image

Wani lokaci, sa'ad da mutane ba su da ruwan sha, Allah ya cewa Musa, "Yi magana ga dutsen, sai ruwa ya fito." Amma Musa ya ƙasƙantar da Allah a gaban mutane da ya bugi dutsen sau biyu da sandarshi maimakon ya yi masa magana kawai. Ruwa ya fito daga dutsen domin kowa ya sha, amma Allah ya yi fushi da Musa har ya ce, "Ba za ka shiga ƙasar alkawali ba."

Image

Bayan da Isra'ilawa suka yi yawo cikin jeji shekara arba'in, duk waɗanda suka yi wa Allah tawaye suka mutu. Sai Allah ya bida mutanen kusan ƙasar alkawalin kuma. Musa fa ya tsufa, sai Allah ya zaɓi Joshuwa ya taimake shi yin jagorar mutanen. Da kuma, Allah ya yi wa Musa alkawali zai aiko wani annabi kamar Musa.

Image

Sai Allah ya cewa Musa jeka bisan ƙolin dutsen domin ka ga ƙasar alkawalin. Musa ya ga ƙasar amma Allah bai yardar mashi ya shiga ba. Sai Musa ya mutu, kuma Isra'ilawa suka makoki kwana arba'in. Joshuwa ya zama sabon jagoransu. Joshuwa jagora ne mai kyau sabili da ya gaskanta da Allah, ya kuma yi masa biyayya.

Labarin LMT daga Fitowa 16-17; Lissafi 10-14; 20; 27; Kuɓowar Shari'a 34