(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

26. Yesu Ya Fara Aikinsa

Image

Bayan da ya ci nasara da jarabobin Shaiɗan, Yesu ya koma da ikon Ruhu Mai Tsarki garin Galili inda yake zaune. Yesu ya yi tafiya daga wani wuri zuwa wani wuri yana koyaswa. Kowa yana zancen shi da kyau.

Image

Yesu ya je garin Nazarat inda ya zauna lokacin yana matashi. Ranar Asabar ya tafi wurin sujada. Suka bashi littafin annabi Ishaya don ya yi karatu. Yesu ya buɗe littafin, kuma ya karanta wa mutanen daga cikinsa.

Image

Yesu ya karanta, "Allah ya ba ni Ruhunsa domin in shaida wa matalauta bishara, saki ga ɗauraru, in buɗewa makafi ido, in ƴantas da wanda suke a ɗanne. Wannan ce shekarar ƙarbuwa ga Ubangiji."

Image

Sai Yesu ya zauna a ƙasa. Kowa yana kallonsa a kusa. Sun san labarin littafin adini da ya karanta yana ambatar Almasihu. Yesu ya ce, "Maganar da na karanta tana faruwa da ku a yanzu." Dukan mutane suka yi mamaki suka ce, "Ba shi ne ɗan Yusufu ba?"

Image

Sai Yesu ya ce, "Gaskiya ne ba annabin da ake mutuntawa a garinshi. Lokacin annabi Iliya, akwai mata da yawa da mazansu suka mutu a Isra'ila. Amma lokacin da ba a yi ruwan sama ba har shekara uku da rabi, Allah bai aiki Iliya ba don ya taimaki gwauruwa ta Isra'ila, amma ya taimaki gwauruwa ta wata kabila."

Image

Yesu ya ci gaba da cewa, "Kuma zamanin annabi Elisha akwai kutare da yawa a Isra'ila. Amma Elisha bai warkar da su ba. Ya warkas da kuturtar Na'aman kaɗai, shugaban yaƙin abokan gaban Isra'ila. Mutanen da suke sauraron Yesu Yahudawa ne. To da suka ji shi yana faɗin wannan sai suka husata.

Image

Mutanen Nazarat suka janye Yesu waje daga wurin sujada, kuma suka kai shi bayan gari suka jefas shi suna neman kashe shi. Amma Yesu ya ratsa cikin jama'a, kuma ya bar garin Nazarat.

Image

Sai Yesu ya yi tafiyarsa zuwa wani gari a Galili, kuma sai taro mai yawa suka zo gareshi. Suka kawo marasa lafiya da yawa da nakassasu, har da makafi, guragu da baibaye, kuma Yesu ya warkar da su.

Image

Mutane da yawa masu aljannu, aka kawo su wurin Yesu. Da faɗar Yesu, aljannun suka fita daga mutanen, suka kuma furta, "Kai ne Ɗan Allah!" Mutanen taron suka yi mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah.

Image

Sai Yesu ya zaɓi mutum goma sha biyu da ake kira manzanninsa. Manzannin suka yi tafiya da Yesu, kuma suka koya daga gareshi.

Labarin LMT daga Matiyu 4:12-25; Markus 1:14-15, 35-39; 3:13-21; Luka 4:14-30, 38-44