(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

50. Yesu Ya Koma

Image

Kusan shekaru 2,000 mutane da yawa cikin duniya suka ji bisaharar Yesu Almasihu. Ekklisiya ta ci gaba da girma. Yesu ya alkawalta zai sake dawowa a ƙarshen duniya. Ko da yake bai komo ba tukuna, zai cika alkawalinsa.

Image

Lokacin da muke jiran dawowar Yesu, Allah yana so mu yi rayuwa mai tsarki, kuma mai darajanta shi. Yana kuma so mu faɗawa sauran labarin mulkinsa. Yayin da Yesu yake a duniya ya ce, "Almajiraina za su shaida bisharar mulkin Allah ga mutane ko'ina cikin duniya, sa'an nan ƙarshe za ya zo."

Image

Kabilu da dama, har yanzu ba su sami labarin Yesu ba. Kafin ya koma sama, Yesu ya faɗawa Krista su shaida bishara ga mutanen da basu taɓa jin labarin ba. Ya ce, "Ku je ku almajirtadda dukan mutane!" Kuma, "Gonaki sun nuna don girbi!"

Image

Yesu kuwa ya ce, "Bawa bai fi malamin shi ba. Kamar yadda hukumar duniya suka ƙini, za su yi muku azaba kuma su kashe ku sabili da ni. Ko da yake za ku sa wuya cikin duniyar nan, ku ƙarfafa gama Na yi nasara da Shaiɗan, wanda yake mulkin wannan duniya. Idan kun jumre har ƙarshe, sai Allah ya cece ku!"

Image

Yesu ya faɗawa almajiransa wani labari don ya fasarta abin da zai faru da mutane in duniya ta ƙare. Ya ce, "Wani mutum ya shuka iri mai kyau a gonarsa. Sa'ad da yake barci, abokin gabansa ya zo, kuma ya shuka irin ciyawa tare da alkama, kuma ya tafi."

Image

"Da shukar ta tsiro, bayin mutumen suka ce, "Malam, ka shuka iri mai kyau a wannan gonar. Ta me ya sa akwai ciyawa a cikinta?" Malamin ya amsa, "Abokin gaba ya shuka su."

Image

"Bayin suka amsawa malamin su, "Ko za mu cire ciyawa?" Malamin ya ce, "A'a. Idan kun yi haka, za ku cire wasu ƴan alkama kuwa. Ku dakata har lokacin girbi ya yi, sa'an nan ku tara ciyawa tari tari don ƙonawa, amma ku kai alkama cikin sito na."

Image

Almajiran ba su gane manufar labarin ba, sai suka tambayi Yesu ya fasarta masu shi. Yesu ya ce, "Mutumen da ya shuka iri mai kyau wakilin Almasihu ne. Gonar wakilin duniya ne. Irin mai kyau wakilin mutanen mulkin Allah ne."

Image

"Ciyawa wakilin mutanen mugun ne. Abokin gaban da ya shuka ciyawar wakilin Shaiɗan ne. Girbin wakilin ƙarshen duniya ne, kuma masu girbi wakilai mala'ikun Allah ne."

Image

"A ƙarshen duniya, mala'iku za su tara dukan mutanen da suke na mugu, kuma su jefa su cikin wutar ƙiburutu, inda za su yi kuka da ciza haƙora cikin muhimmiyar azaba. Sai masu adalci za su haskaka kamar rana cikin mulkin Allah Ubansu."

Image

Yesu ya kuwa ƙara da cewa zai dawo duniya daidai kafin ƙarshen zamani. Zai dawo kamar yadda ya tafi, kuma zai sami jikin mutuntaka, kuma zai komo cikin gajimare na sama.

Image

Sa'an nan Krista waɗanda suke da rai za su tashi zuwa sama su sadu da sauran Krista da suka tashi daga mattatu. Za su zauna can tare da Yesu. Bayan wannan, Yesu zai zauna tare da mutanensa cikin cikakkiyar salama da haɗin kai har abada.

Image

Yesu ya yi alkawali cewa da zai bayar da rawani ga kowane mai gaskantawa da shi. Za su rayu, kuma su yi mulki da Allah cikin cikkakkiyar salama har abada.

Image

Amma Allah zai shar'anta duk wanda ba ya gaskanta da Yesu ba. Zai jefa su cikin wuta, inda za su yi kuka da cizon haƙora cikin tsoro har abada. Wutar da ba ta ƙare ci, za ta ƙone su kulluyomi, kuma tsutsotsi ba su fasa cinsu ba.

Image

Sa'ad da Yesu ya dawo, zai kamala hallakar Shaiɗan da mulkinsa. Zai jefa Shaiɗan cikin wuta inda zai ƙone har abada, tare da duk wanda ya zaɓa ya bi shi maimakon ya yi biyayya da Allah.

Image

Sabili da Adamu da Hawa'u sun yi wa Allah rashin biyayya, kuma sun sanyo zunubi cikin duniya, Allah ya la'anta ta, kuma ya yanke ya hallaka ta. Amma wata rana Allah ya halitta sabon sama da sabuwar duniya cikakkiya.

Image

Yesu da mutanensa za su zauna a sabuwar ƙasa, kuma zai yi mulki har abada bisan dukan abu mai rai. Zai shafe kowane hawaye, kuma ba za a ƙara yin wahala, ko baƙin ciki, ko kuka, ko mugunta, ko ciwo, ko mutuwa ba. Yesu zai yi mulkin mulkinsa da salama da adalci, kuma zai zauna tare da mutanensa har abada.

Labarin LMT daga Matiyu 24:14; 28:18; Yahaya 15:20, 16:33; Wahayin Yahaya 2:10; Matiyu 13:24-30, 36-42; 1Tasalonikawa 4:13-5:11; Yakubu 1:12; Matiyu 22:13; Ruya ta Yohana 20:10, 21:1-22:21