(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

5. Ɗan Alkawali

Image

Shekara goma bayan da Abram da Saraya suka iso Kana'ana, ba su dai haifu ba tukuna. Sai Saraya ta cewa Abram, "Tun da Allah bai yarda mani in samu ƴaƴa ba, kuma yanzu na tsufa ƙwarai domin haifuwa, to ga baranya ta Hajaratu. Aure ta domin ta haifa mana ɗa."

Image

Sai Abram ya auri Hajaratu. Hajaratu ta haifi ɗa namiji, Abram ya kira sunansa Isma'ilu. Amma Saraya ta cika da kishin Hajaratu. Da Isma'ilu ya kai shekara goma sha uku, Allah ya sake magana da Abram.

Image

Allah ya ce, "Ni ne Allah mai iko duka. Zan yi alkawali da kai." Sai Abram ya rusuna ƙasa. Allah ya ƙara cewa Abram, "Za ka zama uban al'ummai da yawa. Zan ba ka, kai da zuriyarka ƙasar Kana'ana gado. Zan zama Allahnsu har abada. Sai ku yi wa kowane ɗa namiji kaciya."

Image

"Matarka Saraya za ta haifi ɗa–zai zama ɗan alkawali. Raɗa mashi suna Ishaku. Zan yi alkawali da shi, zai zama babbar al'umma. Zan sa Isma'ilu shi zama babbar al'umma shima, amma alkawalina da Ishaƙu ne." Sai Allah ya canza sunan Abram, ya kira shi Ibrahim wato ma'ana "uban da yawa". Allah ya kuma canza sunan Saraya ya kirata Saratu, wato ma'ana ƴar sarki.

Image

Wannan rana Ibrahim ya yi wa duk ƴaƴa maza kaciya a gidansa. Kusan shekara guda bayan wannan, lokacin da Ibrahim ya kai shekara ɗari, Saratu shekara tasa'in, Saratu ta haifa ma Ibrahim ɗa. Sun kira shi Ishaƙu kamar yadda Allah ya faɗɗamasu.

Image

Da Ishaƙu ya zama saurayi, Allah ya jaraba bangaskiyar Ibrahim cewa, "Ɗauki Ishaƙu, ɗanka makaɗaici, ka miƙa shi hadaya a garaini." Kuma Ibrahim ya yi biyayya ga Allah, sai ya shirya ya bada ɗansa hadaya.

Image

Lokacin da Ibrahim da Ishaƙu suka zo wurin hadaya, Ishaƙu ya yi tambaya, "Baba, muna da itace don hadaya, amma ina ragon?" Ibrahim ya amsa, "Allah zai tanada wa kansa ragon hadaya, ɗana."

Image

Da suka kawo wurin hadaya, Ibrahim ya ɗaure ɗansa Ishaƙu, ya ɗora shi bisan bagadi. Yana shirin kashe shi sai Allah ya yi magana, "Dakata! Kar ka yanka shi! Yanzu na sani kana tsorona, da yake ba ka ƙi ka ba ni ɗanka, tilonka."

Image

Kusansu Ibrahim ya ga rago cikin kurmi. Allah ya tanada wannan rago don hadaya maimakon Ishaƙu. Ibrahim ya yi hamzari ya miƙa ragon hadaya.

Image

Sai Allah ya cewa Ibrahim, "Domin kana da himma ka ba ni komi, har da ɗanka tilonka, Na yi alkawari in albarkace ka. Zuriyarka za su wuce taurarin sama. Domin ka yi biyayya da ni, dukkan iyalai duniya za su sami albarka ta wurin iyalinka."

Labarin LMT daga Farawa 16-22