(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

30. Yesu Ya Ciyas da Mutane Dubu Biyar

Image

Yesu ya aike da manzaninsa da su yi bishara, kuma su koyas da mutane da yawa a ƙauyuka dabam-dabam. Da suka koma inda Yesu yake, suka faɗa mashi abin da suka yi. Sai Yesu ya gayace su su je tare da shi wani wuri mai kwanciyar hankali kusa da tafki, su huta ɗan lokaci. Sai suka shiga cikin jirgin ruwa, kuma suka ratsa wancan shashen tafki.

Image

Amma akwai mutane da dama da suka ga Yesu da almajiransa sa'ad da suka bar jirgin. Waɗannan mutanen suka gudu ta bakin ruwan su je wancan gefen a gabansu. Sai sa'ad da Yesu da almajiran suka iso, taron mutane da yawa suna shirye, suna jiransu a can.

Image

Taron mutanen ya fi mutum 5,000, banda mata da yara. Yesu ya ji juyayin mutanen. Ga Yesu, wannan mutanen suna kama da tumaki marasa makiyayi. Sai ya koyas da su, kuma ya warkas da marasa lafiya da suke cikinsu.

Image

Da daɗewa cikin rana, almajiran suka faɗa wa Yesu cewa, "Dare ya yi, kuma babu garuruwa a kusa. Aika mutane su je su nemi abinci."

Image

Amma Yesu ya faɗawa almajiran, "Ku, ku ba su wani abu su ci!" Suka amsa masa, "Ƙaƙa za mu iya wannan? Brodi biyar da ƙananan kifi biyu kaɗai garemu."

Image

Yesu ya faɗawa almajiran da su cewa matanen su zauna a kan ciyawa a ƙasa cikin gungun mutane hamsin-hamsin.

Image

Sai Yesu ya ɗauki brodin biyar da kifin biyu, ya ɗaga kai sama, kuma ya godewa Allah domin abincin.

Image

Sai Yesu ya karya brodin da kifin cikin guntaye. Ya ba almajiran gutsuren su rabawa mutane. Almajiran suka yi ta miƙa abincin, kuma bai ƙare ba! Dukan mutane suka ci, kuma suka ƙoshi.

Image

Bayan wannan, almajiran suka tattare abincin da ba a ci ba, kuma ya isa ya cika kwando goma sha biyu! Dukan abincin ya fito daga brodi biyar da kuma kifi biyu.

Labarin LMT daga Matiyu 14:13-21; Markus 6:31-44; Luka 9:10-17; Yahaya 6:5-15