(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

46. Bulus Ya Zama Krista

Image

Shawulu shi ne saurayin da ya riƙe rigunan mutanen da suka kashe Istifanas. Ba ya gaskanta da Yesu ba, sai ya tsanantawa masu bi. Ya je gida zuwa gida a Urshalima don ya kama duk maza da mata, kuma ya sa su cikin kaso. Babban firist ya baiwa Shawulu izinin ya je garin Dimashƙu ya kama masu bin Yesu can kuma ya maido su Urshalima.

Image

Sa'ad da Shawulu yake kan hanya zuwa Dimashƙu, haske mai ƙarfi daga sama ya haskaka kewaye da shi, sai kuwa ya faɗi ƙasa. Shawulu ya ji wani yana cewa,"Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?" Shawulu ya tambaya, "Wane ne kai Malam? Yesu ya amsa masa, "Ni ne Yesu. Kana tsananta mini!"

Image

Da Shawulu ya tashi, ba ya gani. Abokansa suka ja masa gora zuwa Dimashƙu. Shawulu bai ci bai sha ba har kwana uku.

Image

Akwai wani almajiri a Dimashƙu mai suna Hananiya. Allah ya ce masa, "Je gidan inda Shawulu yake, Ɗaura masa hannuwa domin ya samu ganin gari kuma." Amma Hananias ya ce, "Malam, na ji yadda wannan mutumen ya tsanantawa masu bi." Allah ya amsa masa,n "Je ka! Na zaɓe shi ya shaidawa Yahudawa da mutanen wasu kabilu sunana. Zai sha wahalar abu da yawa sabili da sunana."

Image

Sai Hanania ya je wurin Shawulu, ya ɗaura masa hannuwa, kuma ya ce, "Yesu, da ya bayyana gareka a hanya zuwa nan, ya aiko ni wurinka don sami ganin gari, kuma ka cika da Ruhu Mai Tsarki." Shawulu nan da nan ya samu ganin gari, kuma Hananias ya yi masa baftisma. Sai Shawulu ya ci ɗan abinci, kuma sai ƙarfinshi ya dawo.

Image

Nan take Shawulu ya fara wa'azi ga Yahudawa a Dimashƙu cewa, "Yesu Ɗan Allah ne!" Yahudawa suka yi mamaki cewa da mutumen da ya so ya hallaka masu bi, yanzu shima ya bada gaskiya ga Yesu! Shawulu ya kwatamta wa Yahudawa Yesu ne Almasihu.

Image

Bayan kwanaki da yawa, Yahudawa suka tsara su kashe Shawulu. Sai suka aika mutane su tarbe shi a ƙofofin garin don su kashe shi. Amma Shawulu ya ji labarin dabarar, kuma abokansa suka taya shi ya tsira. Wani dare suka sauko shi cikin kwando da igiya daga katangar garin. Bayan da Shawulu ya kuɓuta daga Dimashƙu, ya ci gaba da wa'azi a kan Yesu.

Image

Shawulu ya tafi Urshalima don ya gana da almajiran, amma sun ji tsoronsa. Sai wani mai bi mai sunan Barnabas ya kai Shawulu wurin manzanni, kuma ya faɗa masu yadda Shawulu ya yi wa'azi gagarumi cikin Dimashƙu. Bayan wannan, almajiran suka ƙarɓi Shawulu.

Image

Wasu masu bi da suka gudu daga tsanani cikin Urshalima suka tafi nesa zuwa wani gari Antakiya, kuma suka yi wa'azi a kan Yesu. Yawancin mutanen Antakiya ba Yahudawa ba ne, amma a karin fari, da yawa daga cikinsu kuwa suka bada gaskiya. Barnabas da Shawulu suka tafi can su koyas da sababbin tuba a kan Yesu, kuma su ƙarfafa Ekklisiya. A Antakiya ne masu bin Yesu aka fara kiransu "Krista."

Image

Wata rana, sa'ad da krista a Antakiya suke azumi da addu'a, Ruhu Mai Tsarki ya ce masu, "Ku keɓe mani Barnabas da Shawulu su yi aikin da na aike su, su yi. Sai Ekklisiya cikin Antakiya suka yi addu'a domin Barnabas da Shawulu, kuma suka ɗaura masu hannuwa. Sai suka aike su, su yi wa'azin bisharar Yesu a waɗansu wurare da yawa. Barnabas da Shawulu suka koya wa mutane na kabilu iri- iri, kuma mutane da yawa suka gaskanta da Yesu.

Labarin LMT daga Ayyukan Manzanni 8:3; 9:1-31; 11:19-26; 13:1-3