(Hausa) هَوُسَ: Open Bible Stories

Updated ? hours ago # views See on DCS

43. Ekklisiyar Farko

Image

Bayan da Yesu ya koma sama, almajiran suka tsaya a Urshalima kamar yadda Yesu ya umurce su. Masu bi a can suka riƙa taruwa tare domin addu'a.

Image

Kowace shekara, kwana hamsin bayan Idin Ƙetarewa, Yahudawa suna yin wata babbar sallah da ake kira Fentikos. Fentikos lokaci ne da Yahudawa suke idin girbin alkama. Yahudawa suka zo daga ko'ina cikin duniya domin su yi Fentikos tare. Wannan shekara, lokacin Fentikos ya zo daidai da sati guda bayan da Yesu ya koma sama.

Image

Sa'ad da masu bi suke tare, ba zato ba tsammani, gidan da suke ciki ya cika da ƙara kamar na iska mai ƙarfi. Sai wani abu kamar harsunan wuta suka bayyana bisan kanun dukan masu bi. Duka suka cika da Ruhu Mai Tsarki, kuma suka fara magana da waɗansu harsuna.

Image

Da mutanen Urshalima suka ji muryoyin, taron jama'a ya zo ya gani mai ke faruwa. Da mutanen suka ji masu bin suna shelar al'ajabai ayyukan da Allah ya yi, sai suka yi mamakin abin da ya faru, suna jin maganganun kowane cikin harshensu.

Image

Waɗansu mutanen suka zargi almajiran cewa da sun bugu da giya. Amma Bitrus ya tashi ya ce masu, "Ku saurare ni! Wannan mutane ba su yi maye ba! Wannan ya cika annabci da annabi Yowel ya yi cikin wanda Allah ya ce, 'Cikin kwanakin ƙarshe, zan zubo da Ruhuna.'"

Image

"Mutanen Isra'ila, Yesu mutum ne wanda ya yi babbar shaida, kuma ya yi al'ajabai da yawa da ikon Allah, kamar yadda ku ka gani, kuma kun riga kun sani. Amma ku ka giciye shi!"

Image

" Ko da yake Yesu ya mutu, Allah ya tashe shi daga mattatu. Wannan ya cika annabcin da ya ce,'Ba za ka bar mai Tsarkin ka ya ruɓe a cikin kabari ba.' Mu shaidu ne cewa Allah ya tada Yesu zuwa rai kuma."

Image

"Yesu yanzu ya kimantu a hannun dama na Allah Uba. Sai Yesu ya aike da Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi alkawali zai yi. Ruhu Mai Tsarkin ne yake sawa dukan ayyukan da ku ka gani ko ji, su faru."

Image

"Kun giciye wannan mutumen, Yesu. Amma ku sani da cewa hakika Allah ne ya sa Yesu ya zama Ubangiji da Almasihu!"

Image

Mutanen da suke sauraron Bitrus sun taɓu sosai da abin da ya ce. Sai suka tambayi Bitrus da almajiran,"Ƴan'uwa, me ya kamata mu yi?"

Image

Bitrus ya amsa masu, "Kowanen ku sai ya tuba, kuma a yi masa baftisma cikin sunan Yesu Kristi domin Allah ya gafarta zunubinku. Kuma zai kuwa ba ku kyautar Ruhu Mai Tsarki."

Image

Kusan mutane 3,000 suka bada gaskiya ga faɗawar Bitrus, kuma suka zama almajiran Yesu. Aka yi masu baftisma, sai suka zama membobin Ekklisiya a Urshalima.

Image

Almajiran suka ci gaba da sauraron koyaswar manzannai, suka ci lokaci tare, suka ci abinci tare, kuma suka yi wa juna addu'a. Suka yi murnar yabon Allah tare, kuma suka raraba kominsu tsakanin juna. Kowa ya yaba masu. Kowace rana mutane masu bi suka yi ta ƙaruwa.

Labarin LMT daga Ayyukan Manzanni 2